Majalisar Dattawa ta ragargaji Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari, dangane da wasu kalamai da aka ce ya furta kan batun matsalar man fetur.
A cikin wata takardar da aka raba wa manema labarai, kakakin yada labarai na majalisa, Sabi Abdullahi, ya ce Abba Kyari bai yi dattako ba da aka ce ya dora laifin matsalar mai kan Majalisar Dattawa ce da laifi saboda ta dauki lokaci mai tsawo ba ta sa hannun amince wa Shugaba Buhari ranto kudade wasu kudade ba.
PREMIUM TIMES dai ba ta da tabbacin hujja ko wata shaidar cewa Abba Kyari ya fadi maganar, sannan kuma an yi kokarin jin ta bakin sa ko bakin kakakin yada labaran sa, amma ba a yi nasara ba.
An kuma tun tubi Kakakin Yada Labaran Shugaban Kasa, Femi Adesina, amma ya ce a bai san da labarin ba.
Discussion about this post