Maida hankali wajen gyara asibitocin kasar nan ne mafita -Likita Titus

0

Wani kwararren likitan kunne,hanci da makogoro a asibitin koyarwa na jami’ar Abuja Titus Ibekwe ya ce gurbacewar fannin kiwon lafiyar kasar nan da yadda mafi yawan mutanen kasar ke fita kasashen waje neman ingantaciyyar kiwon lafiya na daga cikin dalilan da ya sa kasa ke asarar miliyoyin kudade.

Sakamakon haka ne ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da kudurorin da za su taimaka wajen hana mutane fita kasashen waje neman kiwon lafiya.

Ya ce maida hankali wajen saka jari a fannin kiwon lafiyar kasar nan domin farfado da ita ne kawai mafita.

Share.

game da Author