Wasu mahara sun kai hari kauyen Iware, dake Jada , inda suka kashe mutane tara sannan suka sace yara bakwai.
Wani dan banga da ke zaune a garin yace bayan wannan hari, maharan sun shiga wani kauye kusa da wannan gari inda suka kashe mutanen wani gida su tara kaf.
“ Ayyukan mahara ya dawo yanzu. Sukan biyo dare ne su yi ta kashe mutane suna sace ya’yan mu da shanu, daga baya su kira domin karba kudin fasa.
“ An sanar da ‘yan banga, ‘yan farauta da sauran jami’an tsaro kuma tuni sun fantsama dazukan mu don farautar wadanda suka aikata wannan aiki.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Othman Abubakar ya bayyan cewa da maharan sun fi aikata wannan mummunar aiki a dazukan Toungo ne amma yanzu sun karkata zuwa Jada da Fufore.”
Idan ba a manta ba kwanakin baya an taba sace dan uwan tsohon shugaban hukumar EFCC, Sani Ribadu da wasu yan uwan wasu jigajigan yan jam’iyyar APC.