Wani ma’aikacin hukumar gudanar da bincike kan kiwon lafiya na Najeriya NIMR, Bamidele Iwalokun, ya yi kira ga gwamnati da ta tsananta hana shigowa da magugunan rage kiba kasar nan.
Bamidele ya koka kan haka ne ganin yadda magungunan suka cika kasuwannin kasar nan duk da basu da inganci kuma suna da hadari ga lafiyar mutane.
Daga karshe ya yi kira ga hukumar kula da magunguna da abinci NAFDAC,hukumar tabbatar da ingancin kaya, SON da kuma hukumar su da su wayar da kan mutane game da illolin da ke tattare da amfani da wadannan magunguna.