Kungiyar likitocin Najeriya NMA reshen jihar Kogi sun fara yajin aikin ‘sai baba ta gani’ daga ranar Litini 8 ga watan Janairu.
Idan ba a manta ba kungiyar NMA reshen jihar Kogi sun janye yajin aikin da suka fara yi ne ranar 22 ga watan Yuni 2017 sakamakon alkawuran da gwamnatin jihar ta dauka na biyan duk bukatun su da suka mika wa gwamnatin.
Sakamakon haka ne kungiyar ta amince ta koma aiki sannan ta ba gwamantin wa’adin daga wannan lokaci zuwa ranar 31 ga wantan Disambar 2017.
Shugaban kungiyar Godwin Tijani wanda ya sanar da haka a Lokoja ranar Lahadi ya ce fara wannan yajin aiki ya zama dole saboda kin cika musu alkawuran da gwamnatin jihar ta dauka tun a watan Yulin 2017.
” sakamakon hakan muka amince da fara wannan yajin aikin daga karfe 12 na dare Lahadi.”
Ya ce likitocin za su koma aiki ne idan gwamnati ta fara biyan su albashi da sabuwan tsarin biyan albashi sannan da sauran bashin da suke bin gwamnatin tun Janairu 2014.
Daga karshe Tijani ya mika godiyarsa ga kwamishinonin kiwon lafiya, kudi da kuma sauran mutanen da suka tabbatar kungiyar ta dauki wannan shawaran ba tare da an sami rashin jituwa ba da kuma hakurin da likitocin suka yi.
Discussion about this post