Kungiyar likitocin Barno sun baiwa gwamnatin jihar wa’adin kwanaki 21 ta biya duk bukatun su ko kuma su fara yajin aiki.
Shugaban kungiyar Bukar Abbagana wanda ya sanar da haka wa manema labarai a Maiduguri ya ce kungiyar ta dauki wannan matsayi ne ganin cewa gwamnati ta kasa biyan su albashin su har yanzu sannan ba a ma maganar kudaden alawus din su.
” A lissafe likitoci 150 sun yi shekar 4 suna bin gwamnati kudaden alawus da albashin su da ya kai Naira miliyan 300.”
Abbagana ya ce kwanakin wa’adin da suka bada ya fara ne daga ranar 8 ga watan Janairu zuwa 5 ga watan Fabrairu.
Sannan ya roki mutane, kungiyoyi, masu ruwa da tsaki a jihar da su taya su kai kukan su ga gwamnati domin hana su fara yajin aikin ganin cewa hakan zai jefa mutane cikin wani hali.