Wasu kungiyoyi masu zaman kasu ‘Entrepreneurship Advocacy Initiative’ da ‘Media for Development Initiative’ da ke garin Kaduna sun tallafa wa wata yarinya matashiya mai suna Zainabu Iliyasu da ke sana’ar gyara da hada takalma, mazauniyar Unguwar Bulbula, garin Jos, jihar Filato da kayan aiki domin bunkasa sana’ar ta.
Jagoran tawagar, kuma shugaban kungiyar Media for Development Initiative, Ahmed Maiyaki ya ce kungiyoyin sun yi haka ne ganin irin kwazo da himma da wannan matashiya ta yi wa kanta na zama kallabi tsakanin rawuna.
Yakan zama abin kallo ga jama’a musamman idan aka ga mace haka na ayyuka da ba a saba ganin ‘ya mace na yi ba, musamman gyara ko hada takalma.
Tun bayan wani rahoto da VOA ta yi kan wannan baiwar Allah ne ya ba wadannan kungiyoyi karfin guiwar yin tattaki zuwa garin Jos domin yin ido hudu da wannan yarinya sannan su taimaka mata da kayan aiki.
Ahmed Maiyaki ya ce dole ne kungiyoyi masu zaman kan su su rika yin irin haka domin taimakawa masu karamin karfi.
” Bai kamata ace wai komai sai gwamnati ba. Idan Dambu yayi yawa ba ya jin mai.” Inji Ahmed.
Ita ko wannan badukuwa ta yaba wa wadannan kungiyoyi sannan ta ce hakan zai taimaka wa sana’ar ta matukar gaske.
Abubuwan da aka bata sun hada da Janareto, Injin din goge takalma, keken dinkin, sannan har shagon aiki an kama mata da sauran su.
Discussion about this post