Kungiyar WHO ta amince da ingancin maganin rigakafin cutar ‘Typhoid’

0

Kungiyar kula da kiwon lafiya na duniya WHO ta amince da ingancin sabuwar allurar rigakafin cutar zazzabin ‘Typhoid’ mai suna TCV.

Kungiyar ta gano cewa sabuwar rigakafin na da inganci sannan ya na Kara bunkasa garkuwar jikin mutum fiye da wadanda ake amfani da su a da.

Kungiyar ta ce za a iya wa yara kanana allurar.

Bayan haka kungiyar bada shawara kan alluran rigakafi ‘SAGE’ ta shawarci kungiyar WHO cewa za a iya yi wa yara ‘yan watani sama da 6 alluran rigakafin musamman a kasashen da suke fi fama da wannan cuta.

Share.

game da Author