Jama’atu Nasril Islam, JNI, wadda Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar ke jagoranci, ta fatattaki Kungiyar Kiristoci ta CAN dangane da bayanin da CAN din ta yi kan Musulmi da kuma rikicin Fulani da manoma.
JNI ta ragargaji CAN ne biyo bayan wani taro da manema labarai da sakataren CAN na kasa, Musa Asake ya yi.
Sakataren Jama’atu Khalid Aliyu, ya zargi Asake da kokarin bata addinin Musulunci da Musulmi. A cikin takardar da Jama’atu ta fitar, ta yi nuni da wasu muhimman batutuwa da suka hada:
” Kungiyar Kiristoci ta kware sosai wajen kokarin sai ta muzanta addini, ta hanyar kokarin da kungiyar ke yi wajen cusa siyasar addinanci a duk wani batu da ya taso na kasar nan, musammamn idan ya shafi batu ne da Musulmi a ciki.
” Rabaran Musa Asake, ga shi dai babban malami ne na addinin Kiristanci, amma ashe malamin ba malam ba ne, babu komai a cikin kan sa nuna kiyayya, maida karya ya ce ita ce gaskiya tare da yawan kauce wa koyarwar addinin Kiristanci da ya ke yi.
” Bayanan da Musa Asake ya yi wa ‘yan jarida a ranar 16 Ga Janairu, cike ya ke da karairayi, kokarin haddasa fitina, karkatar da hankulan mutane, muggan kalaman kokarin rikita kasar nan.
” Ba za mu biye masa mu bi shi a cikin toka mu na birgima ba. Amma abin da ya fi damun mu, shi ne irin tulin karerayin da ya rika shekawa kan Musulunci da musulmi.
” Kawai sun ruruta batun makiyaya domin su kirkiro wata mummunar kalma ga daukacin wata kabila su muzanta ta, saboda wata bakar aniyar su ta boye, saboda 2018 ta shigo, sun ga zaben 2019 ya karato.
” Babu abin da CAN ke yi sai tsula tsiyar ruruta wutar siyasa a kasar nan kawai, sun saki addini, sun kuma saki laila sun a bin basha.
” Me zai hana kungiyar Kiritoci ta kasa, CAN ta je ta yi rajista da INEC a matsayin jam’iyyar siyasa. Ta haka ne kawai za su iya gwada yawan mabiyan su ko magoya bayan shirmen da suke yi.
” Mu na sane da yadda ake yawan kama Kiristoci na yin shigar-burtu, a hare-haren Boko Garam. An kama kiriastoci sun kai harin ba ma coci, a cikin shiga irin ta kayan musulmi. Ga batun Lydia Yusuf ta Bauchi, ta Miya da sauran su.
” Ina batun manyan ku limaman Kiristoci masu yada kalaman kiyayya? Ina babban limamin kiristan da ya ce idan an ga Bafulatani musulmi, a kashe shi kawai? Haka Fasto Sulaiman ya fada, shi ma Fasto Adebayo ya fadi haka.
” Yawanci duk wata magana da Bishop Kukah zai yi a kan Musulmin kasar nan, to kalaman kiyayya ne. Kwanan baya ya ce, ‘abu kadan zai hada ka rigima da musulmi sai ya kashe ka.’
Saboda CAN ta ga ta na tsula tsiyar ta an sa mata ido, yanzu kuma ta fito da wani sabon salon tuggun rikita kasar nan. Duk inda kiristoci suka yi kashe-kashe, ba za ta sa wannan kisan a cikin lissafi ba, sai inda Fulani makiyaya su ka yi, to sannan ne kisan ya zama kisa.
Mu dawo batun kashe-kashen jihar Benue. Me ya sa CAN saboda munafurci ta ki yin magana a kan ‘yan ta’addar da aka bada rahoton an kama wadanda gwamnatin jihar ta dauka sojojin-hayar yi mata kisa?
In banda jahilci Sakataren CAN, Musa Asake, ya zai ce wai Fulani sun dauki kan su kabilar da ta fi kowace a kasar nan? Ya kamata ya koma makaranta ya sake bibiyar tarihi. Ga shi da ya na da digirin-digirgir, amma irin digirin da ba shi da amfani.
” Asake, ka sani cewa tun ma kafin Buhari ya hau mulki ana karkashe Musulmi a Arewa ta Tsakiya, Arewa ta Yamma. Ga kisan-kiyashin da aka yi wa Musulmi a cikin 2012 a Dogon Dawa, a Birnin Gwari tun a salar asubahi. Cikin Oktoba, 2014, an kashe sama da 103 a karamar hukumar Faskari, jihar Katsina, ga Zamfara, ga mata da kananan yaran Fulani sama da 90 da aka kashe a karamar hukumar Kajuru, cikin jihar Kaduna a Agusta, 2017. Makasan Kiristocin Adara ne su ka kashe su.
” Ko ka manta da Fulanin da aka kashe a Rugar Alhaji Malam, ga wadanda aka kone a Unguwar Aku, ga wadanda aka daddatsa gunduwa-gunduwa kauyen Malam Yelwa da ke Aguba cikin jihar Kaduna.
In banda jahilcin Musa Asake, ya zai ce wai kashe-kashen da ake yi a Arewacin kasar nan wai jihadi ake yi? Kun ji jahili ko! Shi ba babu komai a kwakwalwar sa sai tsantsar nuna kiyayya da musulmi da musulunci kawai.
” Wato so ka ke mu ma mu ce kashe-kashen da aka rika yi wa Musulmi a Zamfara, Katsina, Birnin Gwari, Mambilla, Adamawa, Borno da Yobe da mummunan kisan da aka rika yi wa Musulmi a Filato duk shirin yada Kiristanci ne kenan?
Wai me ya sa Asake ke kaskantar da addinin Kiristanci ne haka kawai?
” Ku dubi yadda a cikin jawabin sa har ya ke murna da yadda shugaban Amurka Domald Trump ya maida ofishin jakadancin Amurka a Jerusalem. Lallai wannan bai ma san diflomasiyyar duniya ba.
Amma kuma ba mu yi mamaki ba, domin mun san shugaban Nijeriya wanda ya taka rawar hana wa Falasdinawa ‘yanci a cikin 2014.
Sannan kuma ba mu manta ba da yadda aka kama jirgin Shugaban CAN na Nijeriya dauke da tulin daloli ya shiga kasar Afrika ta Kudu cinikin makamai.
MATSAYAR MU GA GWAMNATI: RAN KIRISTA BAI FI RAN MUSULMI DARAJA A NIJERIYA BA
” Mu na yin tir da Allah-wadai da yadda gwamnati ta yi shiru da bakin ta a lokacin da Kungiyar Kiristocin Kisa na Bachama suka kashe Fulani a kauyukan Shawal, Gumara, Kikam da Kandami a jaihar Adamawa a ranar 20 Ga Nuwamba, 2017.
” Mu ma ba mu yarda ba, tilas a fito da makasan da suka kashe Fualanin a hukunta su. An kashe Fulani 87 amma gwamnati ta yi shiru, kuma yawancin su mata ne da kananan yara. An kone musu gidajen su, an kashe dabbobin su.
” Abin takaici da tir shi ne yada jaridu suka ki maida hankali kan wannan kisa.
” Shi ma kisan da aka yi a kauyukan Kunturi daga Girei, Borrog da Luru daga Demsa, Kotumbo daga Numan duk mugun tuggun shafe wata al’umma ce daga doron kasa.
Me ya sa gwamnati duk ta kauda ido daga wadannan kashe-kashen? Ko don musulmi ne aka kashe ne?
” Cikin Yuni, 2017 an yi mummunan kisan kiyashi a jihar Taraba, an kashe kimanin Musulmi 800, amma gwamnati babu ruwanta. Gwamnatin Taraba sai kokari ma ta ke yi a saki wadanda su ka yi kisan.
” To mu ma mu na kira sai a hukunta duk wadanda su ka yi wannan kashe-kashen.
Discussion about this post