Kungiyar Dattawan Arewa ta nada Sani Zangon Daura a matsayin sabon shugaban ta. Hakan ya biyo bayan wani rudanin siyasar cacar-baki da Arewa ko kasar nan su ka shiga, bayan kashe-kashen da aka yi a Benue, Taraba, Adamawa da Kaduna da sauran sassan kasar nan.
Idan ba a manta ba, shugaban kungiyar Pul Unongo ya sauka daga mukamin sa, biyo bayan wani kalami da ya furta wanda a bisa dukkan alamu bai yi wa sauran shugabannin da ma ‘yan Arewa dadi ba.
Unongo ya kuma zargi tsohon mataimakin shugaban kasa da cewa shi ne ke daukar nauyin Kungiyar Miyetti Allah su na kashe mutane a baya-bayan nan.
Bayan wannan kuma ya sake sakin-bakin cewa kabilar su a shirye su ke da su kafa sojojin sari-ka-noke da makamai su yaki Fulani makiyaya.
Tuni dai Atiku ya nemi Unongo ya janye maganar da ya yi ko ya maka shi kotu. Shi Unongu ya karbi shugabancin kungiyar bayan rasuwar marigayi Maitama Sule, Danmasanin Kano.
Kakakin kungiyar Ango Abdullahi ne ya bayar da wannan sanarwa.