KUKAN ’YAN NAJERIYA GA BUHARI: Ka sauka daga mukamin Ministan Fetur kawai

0

Akasarin ’yan Najeriya da suka bayyana ra’ayin su a wata kuri’ar jin ra’ayoyin jama’a da PREMIUM TIMES ta shirya kuma ta gudanar, sun nuna cewa Buhari ba shi da wani zabi a matsayin sa na Ministan Fetur sai ya sauka daga mukamin nasa kawai.

Wannan kiraye-kiraye da su ka yi, ya biyo bayan matsanancin wahala da tsadar fetur da Najeriya ta tsinci kan ta a ciki tun a lokacin bukukuwan Kirismeti, inda har yanzu a yawancin jihohi ana ci gaba da fama da matsalar.

A wannan kuri’ar jin ra’ayoyin jama’a wadda PREMIUM TIMES ta shirya, kashi 67.9 na mutane 6,739, duk sun nuna cewa ya kamata Shugaba Muhammadu Buhari ya sauka daga mukamin Ministan Albarkatun Man Fetur, ya nada wani.

Shekaru biyu da su ka gabata ne Shugaba Buhari ya nada kan sa Ministan Fetur, inda ya nada Ibe Kachukwu a matsayin Karamin Minista.

Buhari ya ce ya bai wa kansa mukamin ministan ne, domin ya samu damar wanke mummunan dattin harkallar da ake yi a harkokin man fetur da suka hada da zamba da satar mai da satar kudade. Ya kuma yi alkawari a lokacin cewa zai kawar da duk wata cuwa-cuwa da kashe-mu-raba da ake yi a ma’aikatar fetur.

YADDA ZABEN YA KASANCE:

Mutane 6,739 ne su ka kada kuri’a, a zaben. An shirya yadda za a yi zaben ne ta yadda bai yiwuwa wani ya jefa kuri’a har sau biyu domin a kwamfuta ko ta wayar selula aka yi zaben a shafin jaridar PREMIUM TIMES.

Tambaya ce aka yi guda daya, wadda ake so a bayar da amsa a lokacin: “Ko ya dace Buhari ya sauka daga mukamin Ministan Fetur?”

Yayin da kashi 66.9 na wadanda su ka yi zaben wato mutane 4,508 kenan, su ka ce ya kamata Buhari ya sauka. Sai kuma kashi 24.5, wato mutane 1,650 su ka nuna cewa kada ya sauka.

Akwai kuma wasu kashi 8, wato mutane 581 da su ka ce su babu ruwan su, ko Buhari ya sauka daga ministan fetur ko kada ya sauka, duk daya.

Share.

game da Author