Ku daina boye ‘yan Boko Haram – Kira ga mazauna Arewa Maso Gabas

0

Rundunar sojin Najeriya ta gargadi mazaunan yankin arewa maso gabashin kasar nan da su daina boye ‘yan Boko Haram a garuruwan su.

Rundunar ta yi kira ga mazauna yankin da su tona asirin duk wanda basu amince da shi ba ofishin jami’an tsaro mafi kusa da su.

Jami’in harka da jama’a na rundunar Sojin Najeriya Janar Sani Kukasheka da ya sanar da haka a Maiduguri yace sun sami rahotanni na sirri cewa wasu ‘yan Boko Haram da askarwa suke fatattaka sun boye a wasu lunguna da yankunan dake garuruwan yankin.

Kukasheka yace duk wanda aka kama ya taimaka wa ‘yan Boko Haram da wurin buya zaidandana kudar sa.

Daga karshe ya yi kira da mazaunan yankin da su ci gaba da ba soji hadin kai don kawar da aiyukkan Boko haram.

Ya ce za a iya kiran su a wannan lambar wayan taraho 193 a duk lokacin da suke bukatan taimakon su.

Share.

game da Author