Kotun dake Igando jihar Legas ta warware auren Gbolahan Olajumoke da matarsa Abimbola Olajumoke bayan rashin zaman lafiya da yaki ci yaki cinyewa tsakanin su, sannan kuma suna zargin juna da yin tsafi tsakanin su.
Gbolahan ya ce matar samasifaffiya ce sannan bata bar har makwabta ba a masifar ta.
Yace sau dayawa kotu ta sha sasanta su amma hakan bai yiwu ba. Da zaran mun fita daga kotu, sai ta koma gidan jiya.
” Bayan haka matata matsafiya ce domin akwai ranar da ta fada min da bakin ta cewa tana zuba min maganin mallake mijji a cikin abinci na da mahaifiyar ta ta bata.”
Duk da wannan zarge-zarge da Gbolahan yake yi wa matar sa ta sa ta musanta haka, tace tun da suka yi aure basu taba yin fada ba a tsakanin su.
Daga karshe alkalin kotun Akin Akinniyi ya warware wannan aure sannan ita matan za ta mayar da kudin sadakin da mijin ta ya biya.
Alkalin ya ce Gbolahan zai biya Abimbola Naira miliyan daya domin ta sami kudin biyan haya sannan ya kuma ce idan kowanen su bai gamu da hukuncin da ya yanke ba zai iya daukaka karan zuwa kotun gaba.