Kotun dake Tinubu a jihar Legas ta daure wani magidanci dan shekara 34 mai suna Bisi Adebiosu a kurkuku sanadiyyar gutsire hancin matar sa da yayi suna fada.
Lauyan da ke kare Bukola, Nurudeen Thomas ya fada a kotu cewa Bisi ya guntule hancin matar sa ne ranar 9 ga watan Janairu.
Ya ce ma’aurantan sun fara samun matsaloli a auren su ne tun bayan matar ta sa ta sami aiki a wani asibiti mai zaman kan ta.
” Duk da cewa Bisi na da shagon siyar da kayan sawa baya kula da iyalen sa sannan kusan kullun sai ya lakada wa matar dukan tsiya.” Inji wanda ya shigar da Kara.
Bisi ya karyata zargin da aka yi masa na dukan matar sa amma ya amince cewa ya gutsire hancin matar sa.
” Na gutsire hancin ta ne cikin haushi saboda a wannan ranar da abin ya faru na dawo na tadda ‘ya’ya na su kadai a gida sannan ita matartawa ta fita ta tafi gantali gidan makwabta.
” Nan da nan sai na harzarta na fita neman ta inda na tsinto ta tsakanin maza ta shan giya.
Bisi ya ce ganin hakan da ya yi sai ya husata sannan ya taso keyanta suka dawo gida. Dawowar su ke da wuya kuwa rikici ko ya kaure. Ana haka ne fa Bisi ya ce fushi ko ya sa ya gutsire mata hanci.
Bayan sauraron su duka alkalin kotun Kikelomo Ayeye ta yanke hukuncin daure Bisi a kurkuku sannan ta daga ci gaba da zaman kotu zuwa 12 ga watan Fabrsiru.