Kotu ta daure mahaifin da ke lalata da ‘yar cikin sa

0

Kotu a Iyaganku ta daure wani kafinta, Olumide Akinleye, mai shekaru 45 a kurkuku da ta kama shi da laifin yin lalata da ‘yar cikin sa da karfin tsiya.

Dan sandar da ya shigar da karar Sunday Fatola ya ce Akinleye wanda ke zaune da ‘yar sa a daki daya a unguwar Odo-Ona Elewa a Ibadan ya fara yin lalata da ‘yar sa ne tun a watan Satumba shekarar 2017.

” Da ‘yar ta gaji da abin da mahaifin ta yake mata sai ta fadawa abokin sa sannan shi kuma ya kawo mana kara a ofishin mu.”

Alkalin kotun Modina Akanni ta yanke hukuncin daure Akinleye a kurkuku har sai an kammala saurarrn karan sannan ta daga zaman kotun zuwa 25 ga watan Janairu.

Share.

game da Author