Sakamakon korar kakkabar ‘ya’yan kadanya da Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ke wa ma’aikatan jihar Kaduna, Kungiyar Kwadago, NLC ta kara jaddada matsayin ta na tir da abin da ta kira bakar aniyar gwamnan Kaduna na korar malamai har dubu 22,000, don kawai ba su ci jarabawa 75 bisa 100 ba.
NLC ta zargi El-Rufai da korar ma’aikatan don kawai ya samu damar ciwo bashi daga bankin Duniya.
Ta bayyana haka ne jiya Labara, inda ta ke nuna goyon baya ga malaman jihar Kaduna, wadanda su ka fara yajin aiki tun a ranar Litinin domin nuna rashin goyon bayan kokar da gwamnan ke kan yi.
Shugaban Kungiyar Kwadago ta Kasa, Ayuba Wabba, ya y i tir da aniyar gwamnatin jihar Kaduna na korar dubban malaman.
Ya ce NLC za ta fara zanga-zanga daga gobe Alhamis, domin nuna rashin goyon bayan abin da ya kira bakar aniyar gwamnatin jihar Kaduna a karkashin El-Rufai.
Ya ce kuma kungiyar za ta kare ‘yancin ma’aikatan da wannan korar ta shafa.
“Watau mun ga cewa duk wata hanyar da ya kamata a bi domin sasantawa da gwamnatin Kaduna, an bi. Amma a karshe mun lura akwai bukatar ko ta halin kaka ne mu taka wa El-Rufai burki ta kowane mataki da doka ta amince, domin mu ceto jihar Kaduna da al’ummar jihar Kaduna daga hannun sa.” Inji Wabba.