Tsohon sanata, mai ra’ayin rikau din jam’iyyar APC, John Udoedehe, ya bayyana cewa shi fa bai damu ba zai iya karbar kowane irin mukami Shugaban Kasa Muhammdu Buhari ya nada shi.
Ya kara cewa bai damu ba ko mukamin kwasa ko sharar bola aka ba shi, karba zai yi.
Idan ba a manta ba, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi nade-naden shugabannin hukumomin gwamnatin tarayya, inda har aka nada Sanata Udoedehe a matsayin shugaban Hukumar Inganta Hanyoyin Fasahar Yada Labarai.
Sanatan wanda ya fio daga jihar Akwa Ibom, ya bayyana cewa tun daga ranar da aka bayyana sunan sa, ya na ta samun kiraye-kiraye daga jama’a da dama cewa ya yi watsi da mukamin, domin ba wani abu ba ne sai cin fuska a wurin sa.
Ya ce wai suna ganin mutum mai karfin fada-a-ji a siyasa kamar sa, bai kamata a kaskantar da shi a bashi wannan mukamin ba.
“Ai idan na ki karbar mukamin tamkar na ci wa Shugaban Kasa fuska ne. Don haka ni mutum ne mai biyayya ga jam’iyya. Ba za ni yi hakan ba.” Haka ya shaida wa PREMIUM TIMES.
“Idan Shugaban Kasa ya duba ya ga cewa ni ne ma na fi dacewa da zama mai sharar bola ko mai goge-goge, to zan karba hannu biyu cikin farin ciki.