KIRA GA SHEHU SANI: Ka dawo PDP kawai, ka rabu da APCn nan – Inji Sanata

0

Sanata mai wakiltan Bayelsa a majalisar dattawa ya bayyana cewa jam’iyyar PDP a shirye take ta karbi Sanata Shehu Sani idan da zai dawo jam’iyyar.

Sanata Ben Bruce ya ce Shehu Sani na daga cikin ‘yan Najeriya kadan da suka rage dake da hangen nesa a kasar nan. Sannan ya zagaya kasar nan lungu-lungu amma irin su Shehu Sani kadan ne suka rage.

Idan Jam’iyya APC bata kaunar sa, tabbas mu PDP na kaunar sa.

Ya fadi hakan ne a shafin sa na twita yau Litinin.

Share.

game da Author