KIRA GA KIRISTOCIN NAJERIYA: Kowa ya shiga siyasa gadan-gadan, Inji CAN

0

Shugaban kungiyar addinin Kiristocin Najeriya Samson Ayokunle yayi Kira ga mabiya addinin kirista na kasar nan da su shiga harkar siyasar Kasar nan gadan-gadan.

Ya ce duk wani da yake bin addinin kirista ya zama masa dole ya shiga sannan a dinga damawa dashi a siyasar Najeriya yanzu.

Samson ya ce maganar nuna halin rashin ko-in-kula da kiristoci ke yi ya kare daga yanzu. “Kowa ya fito ya shiga jam’iyya kamar yadda dokar kasar nan ta gindaya.”

Idan har muna so mu gyara kasar nan to dole ne mu fito my shiga siyasa, ana damawa da mu. Mu zauna muna zuba Ido kamar da ba namu bane yanzu.

Share.

game da Author