KIRA GA BUHARI: Kada Ka kuskura kace za Ka sake tsaya wa takara a 2019 – Inji Father Mbaka

0

Babban Faston Cocin Katolika, Father Mbaka, ya gargadi shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Kada ya kuskura ya ce zai sake tsaya wa takara a 2019.

Mbaka ya fadi haka ne a taron gangami na mabiya darikar Katolika, a Enugu a addu’ar shiga sabuwar Shekara.

” An yi mini bushara da in baka shawara Kada Ka kuskura Ka sake tsaya wa neman takara a karo na biyu a kasar nan. Ka tattara naka-ina-ka ka koma gida hankalin ka kwance ya fi maka.

” Ka dawo cikin hankalin ka, Idan ba haka ba kuwa to, za a ko fidda kai daga ofis kana ji kana gani. Wadanda suke zuga ka ka sake fitowa takara makiyan ka ne kuma Ka sani sune suke kulla maka makarkashiya domin su kunyata ka a idanuwar jama’a.

Idan ba a manta ba, Mbaka na daga cikin na gaba-gaba da suka yaki Jonathan a 2015 sannan suka nuna soyayyar su ga Buhari.

Ya ce Buhari da kan sa ya kirkiro wa Kan sa Matsalolin da ya ke fama da su.

” Allah ya baka mata mai hangen nesa, mai sanin ya kamata, mai baka shawara na gari, amma baka sauraron ta. Wannan mata bata Jin dadi saboda ta san ba mijin da ta sani bane.

Ya ce Idan har Buhari bai mike tsaye ba, wani zai zo ya kwace Wannan kujera ya na gani na abin da zai iya yi.

” Ko Buhari ya canza salon shugabancin sa ko kuma ya dandana kudar sa. Ya canza wadannan miyagun mutanen da suka sarkale shi, ya saka wadanda suka cancanta. Idan ba haka ba kuwa yana gani wata goguwar canjin, zata canza canjin sa. Dama can shine ya kawo wannan canji.

Mbaka ya kara da cewa kusan duka shirye-shiryen gwamnatin Buhari, akwai son kai a ciki.

” An riga an shammaci Buhari, wasu na jujjuya shi yadda suke so.” Inji Father Mbaka.

Share.

game da Author