A yau ne kwamishinan kiwon lafiya na jihar Kebbi Umar Kambasa ya yi wa mutanen jihar albishir din cewa gwamnati ta siyo na’urorin gwaji wa manyan asibitocin jihar 14.
Ya ce gwamnati ta siyo na’urorin ne domin bunkasa kiwon lafiya a jihar.
Ya kara da cewa asibitocin da suka fi bada karfi wajen kula da kiwon lafiyar mata da yara musamman na karkara ne za su fara samun na’urorin. Sannan ya kara da cewa gwamnati ta yi haka ne don ganin an sami raguwa na mutuwar yara kanana da mata.
Bayan haka sakataren ma’aikatan kiwon lafiya a jihar Halima Boyi ta yi kira ga shugabanin asibitocin da za su amfana da wadannan na’urori da su tabbatar sun yi amfani da su yadda ya kamata.
Sannan darektan aiyukkan kiwon lafiya Aminu Bunza y ace za su yi iya kokarin su wajen ganin sun kula da wadannan na’urorin.
Discussion about this post