Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna Austin Iwar ya bayyana cewa tskanin ranakun 20 ga watan Oktoba 2017 zuwa 25 ga watan Janairu 2018 rundunar sa ta kama masu aikata miyagun aiyukka a jihar da suka kai 38.
Ya sanar da haka ne da yake zantawa da manema labarai a Kaduna a yau Laraba.
” Daga cikin mutane 38 din da muka kama 21 daga cikin su masu sace mutane ne da ‘yan fashi da makami sannan sauran 17 kuwa ‘yan sara suka ne. Sannan mun kuma kama wadannan mutane ne da makamai dabam dabam 41 da motoci uku.”
” Cikin wadanda muka kama sun hada da wanda suke aiki a kananan hukumomin Lere, Kubau da Zariya sannan da kewayen Panbeguwa. Sannan mun kuma kama wasu ‘yan sara suka a Rigasa, Tudun-Wada, Kawo da Unguwar Rimi a Kaduna.”
Ya ce wadanda suka kama din na taimaka musu da bayanai wajen gudanar da binciken da suke yi, sannan da bayan haka za su kai su kotu.
Daga karshe Iwar yace rundunar su a shirye take don ganin ta kawar da miyagun aiyukka a jihar sannan ya yi kira ga mutane da su ci gaba da basu hadin kai don samin nasara kan abin da suka sa a gaba.”