JIRGI DANKARE DA MAKAMAI: Jita-jita ce kawai, Inji Kwamishinan ‘yan sandan Taraba

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Taraba ta karyata jita-jitan da ake ta yadda wa wai wani jirgin sama ta sauka a filin jiragen saman jihar dankare da makamai.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar David Akinremi wanda ya karyata wannan jita-jitan yace sun bincike gaskiyar wannan magana in da suka tafi filin jirgin don gani wa idanuwar su, sai suka gano cewa ba haka bane.

Bayan haka rundunar ta ce ta kama mutane tara wanda take zargin da kona ofishin ‘yan sandan dake kauyen Zing.

Daga karshe Akinremi ya yi kira ga mutane da su daina kai wa ofishin su da ma’aikatan su hari sannan ya kuma tabbatar da cewa za su hukunta duk wanda suka kama da aikata irin wannan laifin.

Share.

game da Author