Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana cewa ta rigaya ta kebe fili mai eka 5,300 domin gina makiyayar dabbobi a jihar.
Mashawarci na Musamman ga Gwamna Aminu Masari, mai suna Abba Abdullahi ne ya bayyana haka ga manema labarai yau Alhamis a Katsina.
Abdullahi ya kara a cewa yin hakan wani hobbasa ne da gwamnatin jihar ta yi domin magance fadace-fadacen makiyaya da manoma a jihar.
Ya ce za a kafa makiyayar ce a Gurbin-Baure, cikin Karamar Hukumar Jibiya.