JAMB ta fito da tsauraran sharuddan shiga dakin jarabawa

0

Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a, JAMB, ta tsayar da ranar 9 ga Maris, 2018 ranar da za a yi jarabawar shiga jami’a, ta UTME.

Shugaban hukumar ne, Ishaq Oloyede, ya bayyana haka a wani taro da jiga-gigan hukumar a yau Talata.

An shirya taron ne musamman domin tattauna hanyoyin da za a bi wajen shirya jarabawar.

Oloyede ya ce jarabawar gwajin da aka tsara za a yi a ranakun 22 da 24 Ga janairu, yanzu an daga zuwa cikin makon farko na watan Fabarairu.

Ya kara da cewa dage jarabawar ya biyo bayan yajin aikin da ma’aikatan jami’o’i ke yi a kasar nan.

Sai dai kuma ya kara da cewa har ya zuwa yau kashi 10 bisa 100 ne kadai suka sayi fam na nuna sha’awar su ta rubuta jarabawar. Ya na mai cewa dalibai 283,319 ne kadai suka sayi fam.

TSAURARAN MATAKAI

Duk abin da aka haramta wa dalibi shiga da shi a cikin dakin jarabawa, to an haramta shi ga mai duba su da kuma masu shirya jarabawar.

Ba a yarda dalibi ya shiga da agogo da kyamarar daukar hoto ba. Sai fa fensiri samfurin HB kawai.

Doka ta biyu ta rataya har a kan malaman da ke duba masu rubuta jarabawar da masu tsara ta.

Share.

game da Author