Sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya Shehu Sani ya bi sahun tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo na kira ga shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya hakura da mulki bayan ya kammala shekarun sa a 2019.
Shehu Sani ya ce Buhari ya yi koyi da tsohon shugaban Afrika ta Kudu, marigayi Nelson Mandela, ya hakura ya tarkata komatsen sa ya tafi tun ana Muradin sa.
“ Buhari mutum ne da ke da kyawawan halaye sannan mutum ne mai dattaku da sanin ya kamata, amma kuma dole ne a fadi masa gaskiya musamman a wuraren da ya gaza da inda ya kasa tabuka abin azo a gani.
“ Shugaba Buhari ya nisanta kansa daga ‘yan siyasar bita zaizai da ‘yan kanzagi, ya hakura da mulki haka nan. Ya koma ya huta wa ran sa.
“ Duk wadanda suke ganin cewa Buhari ne Mandelan Najeriya, to ya yi yadda Mandela yayi shima. Yanzu abin da yakamata Buhari yayi shine ya nemo wanda zai gaje shi, mutumin da zai raya Najeriya kuma ya daukaka matsayin kasar nan.
” Dama can ana neman wanda zai bugi kirji ne ya fadi wa Buhari gaskiya komai dacinta domin abin da yake zukatan mutane da yawa ke nan sai dai babu wanda zai iya haka saboda tsoron siyasar sa.
” Kasar nan tana ta tanga-tangal ne yanzu inda saura kadan ta tsaya cak babu gaba babu baya, kabilanci da bambance bambancen addini yayi wa kasa Katutu. Shugaban Kasa ba zai sami shawarar arziki daga wadanda suke manne da shi ba domin suna tare da shi ne saboda siyasar su ne kawai sannan wasun su dashi suka jingini, idan bashi sun kade.
Discussion about this post