HUKUMAR ZABE: Jadawalin Zaben 2019

0

Hukumar Zabe ta fitar da jadawalin ranakun da za a yi zabukan 2019.

Kamar yadda hukumar ta zayyano, za a yi zaben shugaban Kasa da na majalisar tarayya ne ranar 16 ga watan Fabrairun 2019.

Sannan za a yi na gwamnoni da na majalisar dokoki na jihohi ranar 2 ga watan Maris, 2019.

Za a gudanar da zaben fidda dan takara na shugaban kasa da majalisar kasa daga ranar 18 ga watan Nuwamba.

Sannan jam’iyyu da ‘yan takara za su fara kamfen daga 18 ga watan Nuwamba, 2018.

Share.

game da Author