Mataimakiyar Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Amina Mohammed, ta bayyana cewa duk da irin gagarimar nasarar da sojojin Nijeriya su ka yi wajen dakile hare-haren ta’addanci a Arewa-maso-Gabas, to maganar gaskiya ita ce har yau ba a ga bayan Boko Haram ba.
Amina wadda kafin nada ta Shugabancin Majalisar Dinkin Duniya, ita ce Ministar Muhalli ta Shugaba Muhammadu Buhari. Ta ce a wannan sheakara Majalisar za ta taimaki Nijeriya sosai da sosai domin a tabbatar an kara samun gagarimar nasara.
Ta yi wannan jawabi ne a lokacin da ta kai ziyara ofishin Gwamnan Jihar Barno, Kashim Shettima, daidai lokacin da ta kammala ziyarar kwanaki biyu da ta kai jihar.
Ta yaba wa gwamnatin tarayya da ta jihar Yobe musamman ganin irin kokarin da ta yi wajen sake gina al’ummomin da Boko Haram ta yi wa kaca-kaca. Sai ta yi alkawarin kara bayar da tallafi da Majalisar Dinkin Duniya za ta yi domin agaza wa al’ummpmin da Boko Haram ya illata.
Amina ta ci gaba da cewa akwai bukatar kara yin hobbasa wajen inganta hanyoyin da ake taimaka wa sojoji su na gudanar da farmaki kan Boko Haram, musamman a tabbatar su na da kayan fama da suka dace da kuma alaka tsakanin su da fararen hula da sauran hukumomin tsaron kasar nan.
Ta ce yin hakan zai taimaka wa sojoji sanin irin yanayin da wasu jama’a da ke inda aka giggirke jami’an tsaron ke ciki.
“Mun zo Jihar Barno tun shekaranjiya domin mu gane wa idon mu abin da gwamnatin Nijeriya da ta jihar Barno su ka yi da irin tallafin da su ke karba daga Majalisar Dinkin Duniya, domin mu ga nasarorin da aka samar a cikin shekaru biyu da su ka gabata zuwa yau.”
Shi ma gwamna Shettima ya gode wa Mataimakiyar Shugaban Majalisar Dinkin Duniya bisa ga ziyarar da ta kai, ya na mai jaddada cewa zai ci gaba da rubanya irin ayyukan da gwamnatin sa ke gudanarwa domin samar wa al’ummar da Boko Haram ta tarwatsa sauki a rayuwa.
Discussion about this post