Har yanzu muna zaman dar-dar a Benuwai – Ortom

0

Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom ya bayyana wa tawagar gwamnoni 6 da suka ziyarci jihar don yi wa mutanen jihar Jaje da Allah ya kyauta kan kisan wasu ‘yan jihar da ake zargin wasu makiyaya ne suka aikata makonni da suka wuce cewa har yanzu mutanen jihar na zaman tsoro ne.

Idan ba a manta ba shugaba kasa Muhammadu Buhari ya nada kwamiti cikin jagorancin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo domin dubawa da ba gwamnati shawara kan rikice-rikicen fulani da makiyaya da yaki yaki cinye wa.

Ortom ya ce tsoron fulani makiyaya na tare da mutanen jihar sa tun bayan kisan mutane 73 da ake zargin wasu makiyaya ne suka aikata a jihar makonni da suka wuce.

Bayan haka kuma ya ce abin da gwamnati take so shine tunda suna ada hujjojin da ya nuna cewa lallai ga wadanda suka aikata hakan aje a kamo su sannan a hukunta su shine muke kira a yi.

Gwamnonin da suka ziyarci jihar sun hada na Nasir El-Rufai na Kaduna,Kashim Shettima na Barno, Yahaya Bello na Kogi, Badaru Abubakar na Jigawa da Simon Lalong na Filato.

Share.

game da Author