Kakakin gwamna Aminu Tambuwal, Imam Imam ya bayyana cewa gwamnatin jhar Sokoto ta kammala shiri tsaf don horas da malaman Firamaren jihar a musamman fannonin da ya shafi sabbin dabarun koyar wa na zamani don bunkasa ilimi a jihar.
Ya ce malamai daga kananan hukumomi 23 na jihar ne za su sami wannan horo da hukumar kula da ilimi na jihar SUBEB tare da hadin guiwar ‘National Open University of Nigeria, NOUN’ suka shirya.
Imam ya ce za a ci gaba da horas da malaman lokaci-lokaci.
Ya kuma yi kira ga malaman da su sa ido sannan su maida hankali a wannan dama da aka basu domin ci gaban su da karatun firamare a jihar.
Daga karshe shugaban jami’ar NOUN Abdallah Adamu da shugaban hukumar kula da ilimi na jihar Sokoto Bello Danchadi a tsokacin da suka yi sun jinjinawa gwamnan jihar, Aminu Waziri Tambuwal kan mai da hankali da yayi wajen bunkasa fannin ilimi a jihar.
Discussion about this post