Gwamnatin Jihar Kano ta biya bashin naira bilyan daya na bashin da ta gada daga gwamnatin Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda aka kashe wajen sayen man kunna fitilun kan titi.
Kwamishinan Yada Labarai, Muhammed Garba ne ya shaida haka a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a Kano ranar Talata.
Ya ce dukkan kudaden biyan bashi ne na mai da aka saya amma ba a biya ba a lokacin gwamnatin Kwankwaso, aka kunna fitilun cikin birnin Kano, banda sauran garuruwan jihar.
Da bakin kwaminshinan, ya furta cewa a yanzu gwamnatin na kashe naira milyan 125 zuwa 130 wajen sayen mai wanda ake kunna injinan haskaka fitilun kan titi a Kano.