Gwamnatin Kaduna ta sanar da fara daukar kwararrun ma’aikata da suka hada a Lauyoyi 86, Injinioyi, masu zanen gini, da kididdigar gini da wasu kwararru da dama domin cike gurbin wadanda aka sallama da wuraren da ake bukatar aikin kwararru a jihar.
A wata sanarwa da gwamnati ta fitar yau ta ce bayan sallamar ma’aikata da akayi a kananan hukumomin jihar, gwamnati ta kammala shiri domin musanya su da kwararrun ma’aikata.
Kamar yadda sanarwar ta ke, za a dauki lauyoyi 86, da injiniyoyi da dama.
Za a rufe daukar ma’aikatan ne ranar 13 ga watan Faburairu, 2018 sannan za iya cika fom din neman aikin ne a www.kdsg.gov.ng