Gwamnatin ta amince da haka ne bayan shawarar da ta yi da dakarun sojin Najeriya.
Idan ba a manta ba jihar ta kafa dokar hana walwala a jihar daga karfe 8 na yamma zuwa 6 na asuba saboda samar da zaman lafiya a jihar.
Bisa ga sabuwan dokar da aka kafa din dokar za ta fara daga ranar 2 zuwa 6 ga watan Janeru 2018.
Daga karshe gwamnatin ta ce tana fata zata sami goyan bayan mutanen jihar musamman yadda hakan zai taimaka wajen karfafa zaman lafiyan da aka samu a jihar.