Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta samar da dala miliyan daya domin siyo dabarun bada tazaran iyali.
Adewole ya ce ta hanyar wayar da kan mutane mahimmancin amfani da dabarun bada tazaran iyali ne kasar nan za ta sami nasarar cimma burin ta na ganin a yi nasara wajen kyayyade iyali.
Bayan haka Adewole ya ce gwamnati da hadin guiwar kamfanin sarrafa magunguna na ‘May & Baker’ za ta fara sarrafa allurar rigakafi nan da shekaru biyu masu zuwa.
” Domin ganin wannan shiri ya tabbata gwamnati ta kafa kwamiti da zai tsara hanyoyin da za a iya bi don samun nasara a abinda aka sa a gaba.”
Daga karshe Adewole ya ce gwamnati na kokarin kammala shirin ta na ganin cewa dalibai masu yi wa kasa bauta 320,000 sun shiga tsarin inshorar kiwon lafiya a kowani shekara.