Goyon bayan da Buhari ya yi wa shirin gyara ilimi a Kaduna ne ya ingiza El-Rufai – Shehu Sani

0

Sanata dake wakiltan Kaduna ta tsakiya Shehu Sani ya bayyana cewa dalilin goyon bayan da shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba shirin gyaran aikin malunta da gwamnatin Kaduna ke yi ya ingiza gwamnan jihar Nasir El-Rufai wajen korar malamai sama da 21,000 a jihar.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito fili karara a Nuwamba inda ya nuna goyon bayan sa ga shirin da gwamnatin jihar ta yin a sallamar dakikan malamai da suka fadi jarabawar gwaji da jihar.

Shehu Sani ya ce goyon bayan da Buhari ya nuna wa wannan shiri na gwamnatin Kaduna nuni na yi wa ma’aikata tadiyar fin karfi da nuna iko.

Yace hakan da Buhari yayi ya sa gwamnatin jihar na taka malamai da ma’aikatan jihar da yi musu mulkin kama karya da danniya.

Ya yi tir da neman hana kungiyar kwadago gudanar da zanga-zanga a jihar da gwamnati tayi kokarin yi.
“Ina tare da malaman jihar sannan ina goyon bayan zanga-zangar lumana da kungiyar malamaoi da na kwadago suka shirya.
“ Gwamnati bata da Ikon hana zanga-zangar lumana ko kuma matsa ma wani ma’aikaci da ya fito zanga-zanga. Babu dalilin da zai sa a hana wani ma’aikaci fitowa zang-zanga”

“ El-Rufai kamata yayi ya umurci ‘yan sanda su fatattaki Makiyaya da masu garkuwa da mutane ne da suka mai da Kaduna hedikwatar su, ba kungiyoyi, da masu kare hakkin mutane ba. Idan kana jin kai jarumi ne, Fulani makiyaya ya kamata kayi farauta da masu garkuwa da mutane ba ma’aikata da malaman makaranta ba.

Duk da dubban jami’an tsaro da aka jibga a garin Kaduna, kungiyar Kwadago ta gudanar da zanga-zanga a jihar.

Share.

game da Author