GOBARA: Wani magidanci ya rasa ‘ya’ya uku a Jigawa

0

Kakakin rundunar ‘Civil Defence’ na jihar Jigawa Adamu Shehu ya sanar da rasuwar wasu tagwaye da Gambon su sanadiyyar babbakewa a wata Gobara a gidan wani Alhaji Sale Tela dake rukunin gidajen Tudun Tanda a Hadeja.

Shehu ya ce gobarar ta auku ne da misalin karfe 10:45 na daren Lahadi sanadiyyar hardewar wayan wutan lantarki.

Ya ce bayan rasa rayuka da akayi, an rasa dukiyoyi masu yawa.

Daga karshe Shehu ya yi kira ga mutane da su yi hattara da kayan wuta a gidajen su.

Share.

game da Author