Wata gobarar da ta tashi da sanyin asubahin yau Litinin ta lalata gidaje 36, rumbuna 46 da kuma tumakai da awakai 40 a kauyen Abanderi, cikin Karamar Hukumar Dutse, da ke jihar Jigawa.
Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar, Abdu Jinjiri, ya tabbatar da afkuwar gobarar ga manema labarai a Dutse.
Jinjiri, wanda Mataimakin Sufurtanda na ‘Yan Sanda ne, ya ce gobarar ta tashi da misalin karfe 5 na asubahi, wadda ya ce an tabbatar ta tashi ne sakamakon wata wuta da aka kunna a daji.
Sai dai ya kara da cewa, Allah ya takaita gobarar ba ta haddasa asarar rayuka ko daya ba, yayin da ya ce ana nan ana binciken sanadin gobarar.