Gidauniyyar Bill da Melinda Gates za ta biya wa Najeriya bashin Dala miliyan 76

0

Gidauniyyar Bill da Melinda Gates ta amince ta biya wa Najeriya bashin dala miliyan 76 da ta ciyo daga kasar Japan.

Najeriya ta karbo bashin ne don yin amfani da shi wajen ci gaba da yaki da cutar shan-inna da ta keyi.

Ministan kudi Kemi Adeosun ce ta fadi haka ne a Abuja ranar Laraba.

Ta kara da cewa ganin yadda Najeriya ta zage damtse wajen ganin ta kau da cutar ne ya sa gidauniyyar Bill da Melinda Gates ta amince ta biya mata wannan bashi a wannan shekara.

Share.

game da Author