Rundunar Sojojin Najeriya da ke Kaduna, ta kaddamar da shirin kakkabe yawaitar satar mutane, fashi da makami da kuma satar shanu a jihohin Kaduna da Neja.
An saka wa wannan shiri suna ‘Operation Karamin Goro,’ kuma za su karade hanyar Minna-Birnin Gwari-Pandogari, sai kuma hanyar Minna-Sarkin Pawa.
Haka Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a, Muhammad Dole ya bayyana a yau Alhamis.
Kanar Dole, ya bayyana haka a Kaduna, ya na mai yin karin hasken cewa wannan sintiri na su zai hada har da Sojojin Sama, ’Yan Sanda, SSS da kuma dakarun tsaron kasa, wato Civil Defence Corps.
“Yawaitar garkuwa da mutane, fashi da makami da satar shanu na ci gaba da zama babbar barazana ga ‘yan Najeriya.
“Wadannan mugayen masu garkuwa da fashin, su na boyewa ne a cikin surkukin jeji mai duhu da kuma cikin garuruwan da ke kan manyan tituna, sai kuma cikin garuruwan da ke gefen kwalta a cikin daji.
“Saboda barnar da suke yi, jama’a duk sun gudu daga wadannan kananan garuruwa. Don haka ‘Operation Karamin Goro’ zai kakkabe burbudin wadannan ‘yan iska domin a tabbatar da tsaron dukiya da rayukan jama’a.”