FYADE: Kotu ta daure wani matashi a Abuja

0

Kotun karan dake Karshi a Abuja ta daure wani matashi dan shekara 27 mai suna Friday Bamidele a kurkuku saboda samashi da laifin yi wa ‘yar makwabcin sa dake da shekaru 12 fyade.

Lauyan da ya shigar da kara Mahmud Ismaila ya fada a kotun cewa wani makwabcin Friday, Okechukwu Ikechukwu da suke zama a kauyen Jikwoyi ne ya kai karan ofishin ‘yan sandan shekaran jiya, 9 ga watan Janairu.

‘‘Bisa ga karan da Ikechukwu ya shigar cewa a ranar 9 ga watan Janairu Friday ya ja ‘yar makwabcinsa cikin wata ‘yar dajin dake kusa da gidansu inda ya daneta’’.

Kamar yadda aka sanar, shi Friday ya rudi yarinyar ne inda ya kai ta wani daji dake kusa da ita sannan ya danneta karfi da yaji. Bayan haka kuma ya ce mata kada ta kuskura ta fadi wa iyayen ta abin da ya faru.

Ita ko yarinya tana zuwa gida ta fadi wa iyayen ta suko suka kai ta asibiti inda aka tabbatar musu da cewa lallai an kwana da ita.

Yanzu dai kotu ta daure Friday sai 29 ga watan Janairu da za a ci gaba da sauraron karan.

Friday ya musanta wannan zargi da ake masa.

Share.

game da Author