Gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose, ya umarci daukacin Fulanin da ke zaune a jihar, ko ma wace sana’a ya ke yi, to ya yi rajista tare da biyan naira 5,000 kudin rajista.
Yayin da ya ke yi wa Kungiyar Miyetti Allah ta jihar gargadin cewa Fulani su kaurace wa shiga cikin gonakin manoma, Fayose ya ce kowane Bafulatani ya yi kokarin yi rajista cikin watanni uku, ko kuma ya fuskanci fushin hukuma.
Fayose ya gana ne da Kungiyar Miyetti Allah karkashin jagorancin Sarkin Fulanin Jihar Ekiti, Muhammed Abashe da kuma shugabannin kabilun Tivi, a ranar Asabar da ta gabata.
Ya nuna Sarkin Fulani Abashe da yatsa ya ce idan Fulani suka sake kashe wani a jihar, to shi zai sa a kama.
Fayose ya fusata ne sakamakon kisan-ramuwar-gayya da Fulani suka yi kan wata mata kabilar Tiv, bayan kashe wani Bafulani da Tivi suka yi, makonni biyu da suka gabata.
Fayose ya nuna fushin sa ne, ganin cewa ya kira bangarorin biyu ya sasanta su, kuma ya yi rokon kada a sake a yi ramuwar ramuwar gayya, domin za a gano wadanda suka kashe Bafulatanin a hukunta su.
“Duk mai son zama cikin jihar mu, to ya zauna lafiya da mutane. Sannan kuma ku daina shiga gonakin mutane kun a cinye musu amfanin gona.” Inji Fayose.
Ya yi nuni da cewa Fulani su na bata sunan dan’uwan su shugaba Muhammadu Buhari wanda shi ne ke mulkin kasar nan.
Ya kuma ce su na bata sunan sauran Fulani manya a kasar nan, masu mulkin su da kuma dimbin masu ilmin su.
“Mun gaji da kashe-kashe haka nan. Muna son kasancewa a Nijeriya a matsayin kasa daya al’umma daya.”