El-Zakzaky na nan, bai mutu ba, inji lauyan sa

0

Lauyan da ke kare Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, ya bayyana cewa malamin ya na nan bai mutu ba, amma ya na fama da matsanancin ciwo.

Femi Falana ya yi wannan jawabi ne a yau, sakamakon wani labarin da aka fara yadawa a soshiyal midiya cewa El-Zakzaky ya rasu a inda ya ke tsare a hannun mahukuntan gwamnatin Najeriya.

Duk da cewa tun shekaranjiya wata kafar yada labarai ta bogi ta buga labarin, an rika yada labarin mutuwar yau Juma’a awoyi kadan bayan da mabiyan sa su ka kammala zanga-zangar a sake shi a Abuja.

Ana tsare da El-Zakzaky da matar sa tun cikin Disamba, 2015.

Falana ya ce shi da matar sa an bude musu wuta, inda aka ji musu munanan raunuka.

Ya kara da cewa har yau akwai harsashi a cikin jikin matar El-Zakzaky, yayin da gwamnatin tarayya ta hana a fita da su waje domin a yi musu magani.

“A yanzu dai El-Zakzaky da sauran ran sa zan iya cewa, amma rashin lafiya ta kusa cin karfin sa.’’ Inji Falana.

“An fashe masa ido daya, kuma ya ma kusa rasa dayan idon. Ga shi kuma ya gamu da shanyewar sashen jiki a inda aka tsare shi.

“Sannan kuma harsasan da sojoji su ka bude wa matar sa wuta, har yau sun a cikin jikin ta, ba a cire ba, tun 2015.”

Share.

game da Author