El-Rufai ne ya ingiza ‘yan APC su watsar dani – Shehu Sani

0

A maida martani da Sanata mai wakiltan Kaduna ta Tsakiya Shehu Sani ya yi kan amincewa da Uba Sani da ya fito ya yi takarar kujeran sanata a 2019 da shugabannin kananan hukumomi shida suka yi a Kaduna, ya ce wannan abu da akayi ba komai bane illa shiri na gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai.

Ya ce gwamna El-Rufai ya kasa korar sa a jam’iyyar shine ya sa ya tara wai shugabannin APC su amince da wani dan Koran sa.

Ya kara da cewa mutanen Kaduna ta Tsakiya na tare dashi duk da kulle-kullen da gwamnan ya ke yi masa.

” Wannan abu da akayi na wai an yi watsi da Sanata Shehu Sani yanzu, shiri ne na gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai amma ba wani abu.

” Bayan shekaru biyu da rabi na mulkin El-Rufai babu wani abin azo a gani da ya tsinana wa jihar Kaduna.

Shehu Sani ya Kara da cewa El-Rufai ya makalkale wa Buhari don samun mabiya da yin suna a siyasa.

” Ya nada kansa dan takaran gwamnan jihar yanzu kuma ya tura dan Koran sa yin takarar sanata.

Maimakon ya maida hankali wajen samar da zaman lafiya da kare ‘yan Kaduna daga sace-sacen mutane da na ayyukan Makiyaya, kullum ya na fadar shugaban kasa a makale.

Daga karshe ya ce duk wanda ya ke so ya san gaskiyar magana ya zo da kansa ya yi bincike ya gani kafin 2019.

Share.

game da Author