Kungiyar Kwadago ta bayyana cewa babu abin da zai hana ta fitowa zanga-zanga a garin Kaduna gobe.
Kungiyar ta ce jami’an tsaro na ‘yan sanda basu isa su hana su duk da cewa kwamishinan ‘yan sanadan jihar ya yi wa kungiyar kashejin cewa kada su kuskura su gudanar da zanga-zanga a garin domin yin hakan saba wa dokar jihar ne.
Gwamnati ta gargadi mutane cewa kowa ya tabbata ya yi wa kungiyar uwar shegu domin duk wanda ya fito domin tada hankalin jama’ar jihar za a hukunta shi.
A ganawa da manema labarai da kakakin gwamnan jihar Samuel Aruwan yayi da yammacin laraba ya ce kungiyar kwadago basu yi wa gwamnatin jihar adalci ba, domin tun farko da su aka faro shirin yi wa ma’aikatan jihar jarabawar gwajin amma sai gashi yanzu sun nuna kamar ba da su akayi hakan ba.
Bayan haka kuma Kwamishinan ‘yan sandan jihar ya sanar da yammacin Laraban yau, cewa jami’an sa ba za su yi kasa-kasa ba wajen ganin duk wanda ya karya doka a jihar an hukunta shi ba.
Ya ce dokar hana zanga-zanga na nan a jihar Kaduna, saboda haka duk wanda ya karya shi za a hukunta shi.
Yayi kira ga kungiyar kwadagon da ta dakatar da shirin gudanar da zanga-zanga a jihar.
Yanzu dai kowa ya feke wukar sa ana jira.
Discussion about this post