Har zuwa lokacin da muke hada wannan rahoto, bayanan da ya iske mu na nuna cewa tsohon sakataren gwamnatin tarayya David Babachir na shan tambayoyi daga jami’an hukumar EFCC, a ofishin hukumar dake Abuja.
Idan ba a manta an sallami Babachir ne daga aiki bayan fallasa wata badakalar cire ciyawa da ake zargin kamfanonin sa da yi wanda Kwamitin majalisar dattawa ta gudanar a shekarar da ya gabata.
EFCC ta sanar cewa za a ci gaba da yi masa tambayoyi yau Alhamis.
Discussion about this post