Duk da harin da Fulani suka kai kauyukan jihar mu, ba za mu soke dokar hana kiwo ba – Gwamna Ortom

0

A yau ne gwamnan jihar Benue Samuel Ortom ya bayyana cewa wasu makiyaya sun kai hari a kananan hukumomin Guma da Logo inda mutane 20 suka rasa rayukan su sanadiyyar wannan hari.

Ya sanar da haka bayan kammala taro da jami’an taron jihar a Makurdi inda ya kara da cewa maharan sun aikata haka ne tsakanin ranakun Litini da Talata.

Ortom ya ce cikin mutanen da suka rasa rayukan su akwai wasu jami’an kafa dokar hana kiwata dabobi a fili guda 9.

Ya ce bai ga amfanin aikata irin wannan kisan gillan da asarar dukiyoyin mutane da wadannan makiyaya suka yi ba a wannan yankunan.

‘‘Kamata ya yi makiyayan su san da cewa babu fashi game da kafa wannan doka duk da cewa sun aikata hakan a jihar sannan za mu hukunta duk wadanda muka kama da laifin karya wannan doka.”

Ortom ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kirkiro hanyoyin da za abi wajen warware rikicin domin hana Faruwar irin haka nan gaba.

Share.

game da Author