Hamshakin Attajiri, Aliko Dangote, ya gina Tsangayar Koyon Sana’o’i a Jami’ar Bayero, a matsayin gudummawar sa wajen ganin an zaburar da matasa su koyi sana’o’i a matsayin hanyar huce haushin halin matsin tallalin arzikin da ake fama da shi a kasar nan.
Ya gina katafaren sashen ne a matsayin makaranta sukutun, a cikin Jami’ar Bayero, Kano a kan kudi naira bilyan 1.2. za a kaddamar da shi kwanan nan, kasancewa an rigaya an kammala ginin.
Sanarwar da kamfanin Dangote Group ta bayar, ta nuna cewa za a damka ginin a cikin watan Fabrairu ga jami’ar.
Idan ba a manta ba, Dangote ya gina irin wannan makaranta ta koyon sana’o’i a cikin Jami’ar Ibadan, wadda tuni aka kammala ginin ta, sai bude ta kawai ya rage.
Ita makarantar, ta na karkashin kulawar Gidauniyar Dangote ce, wadda kamfanin ya ce irin yadda jama’a suka tsinci kan su ya zama tilas a taimaka da irin wadannan makarantu, domin a inganta rayuwar matasa da nufin koyar da su sana’o’i daban daban irin na zamani.
Da ya ke magana kan wannan gagarimin gudummawa da Dangote ya bai wa Jami’ar Bayero, Shugaban Tsangayar Koyon Sana’o’i ta Dangote, Farfesa Sagagi, a ce babu irin makarantar a cikin BUK, har sai da Dangote ya kawo musu dauki tukunna.
Ya nuna cewa su na tinkaho da alfahari da wannan makaranta, son kowa, kin wanda ya rasa.
Discussion about this post