Kowa dai da abin da ya dame shi a rayuwa musamman a wannan lokaci da neman halaliya ce ta fi zama abin bege ga duk wani ma’aikaci ko magidanci.
A garin Madagali da ke jihar Adamawa, wani abun ban haushi da mamaki da ya faru tsakanin wasu ‘yan sanda kuwa shine yadda saboda wata budurwa mai sai da barasa a wata shaya ta yi dalilin sa saurayin ta wanda Kofur ne a aikin ‘yan sanda ya dirka wa ogan sa wani dan sandan da suke tare a mashayar harsashi.
Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Othman Abubakar ya tabbatar da aukuwan hakan wa PREMIUM TIMES, in da ya kara da cewa abin ya faru ne da misalin karfe 11 na safiyar Talata a gidan giyar.
Shi dai Kofur Bala Adamu ya fusata ne bayan Ogan sa Sajen Emmanuel Timothy ya ki biyan Naira 100 kudin giyar da ya sha daga wajen buduwar sa da ke sai da giyar a mashayar da suke holewa.
” Duk da kin biyan ta kudin giyar da ya sha, Timothy ya zake yana ta dirka mata ashar inda haka ya sa shi ko gogan naka Kofur Adamu ya dirka masa harsashi inda nan take ya sheka lahira.
Abubakar ya kara da cewa yanzu haka sun dauki gawar Timothy zuwa dakin ajiyan gawa na babban asibitin dake Yola sannan shi kuma Adamu an kama shi, zai fuskanci hukuma.