Dan majalisa ya koma APC daga PDP

0

Dan majalisar wakilai dake wakiltar Ileoluji-Okeibo/Odigbo daga jihar Ondo, Akinfolarin Mayowa, ya canza sheka daga jam’iyyan PDP zuwa APC.

Kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara ne ya karanta wasikar sanar da canjin jam’iyyar da Mayowa ya yi a zauren majalisar.

Kamar yadda yake a wasikar Mayowa fadi cewa tun a watan Disamba ya fice daga jam’iyyar PDP sannan kuma tuni ya yi rajista da jam’iyyan APC.

Wannan canza sheka da Mayowa ya yi a majalisan wakilai itace ta farko a wannan shekara.

Share.

game da Author