Gwamnonin jam’iyyar APC sun tsayar da shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sake fitowa takara karo na biyu a 2019.
Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya bayyana cewa gwamnonin sun amince da haka ne ganin cewa shekara hudu kacal bai isa ace Buhari ya kammala abubuwan da ya shirya zai yi wa ‘yan Najeriya ba.
Ya ce sun amince su mara masa baya ne sannan su tabbatar ya zarce domin ya sami cimma burin sa na gyara kasa Najeriya.
Okorocha ya ce dalilin haka ne ya sa muka sake amincewa da minista Sufuri Rotimi Amechi ya zama Darekta janar na Kamfen din na sa a 2019.
Discussion about this post